An kama masu zanga-zanga 11 a London

Fadar Buckingham, London
Image caption Fadar Buckingham, London

'Yan sanda a London sun kame mutane 11 bayan da hatsaniya ta barke ya yi wata zanga-zanga kusa da fadar Buckingham, gidan Sarauniyar Ingila.

Zangar-zangar da kungiyar Anonymous ta gudanar ranar Talata da daddare domin nuna rashin amincewa da matse bakin aljihun gwamnati ta dace da makamantanta da aka gudanar a Amurka, Brazil, Japan da wasu kasashen da dama.

Daruruwan mutane ne dai su ka shiga zanga-zangar ta London.