Majalisa ta amince da karin dokar-ta-baci

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

'Yan majalisar dokokin Najeriya sun amince da bukatar da shugaban kasar ya aike musu ta kara wa'adin dokar-ta-bacin da ke aiki a arewa maso gabashin kasar da watanni shida domin murkushe hare-haren masu kishin Islama.

Baki dayan 'yan majalisar dattawan kasar sun amince da kara wa'adin dokar-ta-bacin a jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.

A watan Mayu ne aka sanar da dokar a jihohin uku a wani bangare na kokarin da gwamnati ke yi na magance hare-haren kungiyar Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad, wanda sanadiyyar haka aka tura dubunnan sojoji zuwa yankin tare da tallafin jiragen yaki.

A wasikar da Mr Jonathan ya aikawa majalisar ya ce rundunar sojin ta samu "kwararan nasarori" akan 'yan bindigar sai dai har yanzu akwai "kalubalen tsaro da suka rage."

Kokwanton tasiri

Sai dai manazarta na da ja game da nasororin da shugaban kasar ke cewa an samu kasancewar har yanzu 'yan Boko Haram din na cigaba da hare-haren da ke hallaka daruruwan fararen hula a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sanatocin ma sun nemi karin bayani game da ingancin ayyukan da sojin ke yi, inda suka ce akwai bukatar shugabannin sojin su gurfana gabansu.

Wani kwararre kan Boko Haram a jami'ar Modibbo Adama da ke Yola, Malam Kyari Muhammad ya ce: "Alamu na nuna an fi kashe mutane a karkashin dokar-ta-bacin idan aka kwatanta da kafin kafa dokar."

Ya kara da cewa kodayake hare-haren da ake cigaba da kaiwa a jihohin Borno da Yobe za su iya zama dalilan kara wa'adin dokar, babu wata gamsasshiyar hujjar da ke nuna dokar ta yi wani tasiri cikin watanni shidan da suka wuce.

Kawo yanzu dai hare-haren sun tashi daga birane zuwa kauyuka amma babu abinda ya rage a hare-haren da ake dangantawa da Boko Haram a adadi, girma ko tsanani.

A jihar Borno dai, har yanzu layukan wayar salula na rufe, abinda sojoji suka ce zai dakushe kaifin hare-haren Boko Haram yayinda manazarta ke cewa hakan na hana mazauna jihar damar neman dauki idan ana kai musu hari.