Mahaukaciyar guguwa a Philippines

'Yan Philippines na gujewa mahaukaciyar guguwa
Image caption 'Yan Philippines na gujewa mahaukaciyar guguwa

Wata mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai karfin gaske da aka yi wa lakabi da Hayan wadda ake ganin tana daga cikin mafiya karfi a tarihi ta sauka a kasar Philippines

A yankunan da ke gabar teku iskar tana gudun kilomita 300 a sa'a daya da zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya kuma torokon igiyar ruwa ya kai tsawon mita 15, wanda hakan ya haddasa gagarumar ambaliya da zaftarewar kasa.

Bishiyoyin da ke faduwa sun kashe hanyoyi, rufin gidaje na kwarewa, gilasan tagogi na ta fashewa, kuma harkar sadarwa da samar da wutar lantarki duk sun katse.

Hukumomi sun ce sama da mutane dubu 120 ne suka sami mafaka a wuraren da aka tanada na musamman.

Karin bayani