Mutane fiye da 100 sun mutu a birnin Tacloban

Ta'adin mahaukaciyar guguwa
Image caption Mahaukaciyar guguwar ta durfafi Vietnam

A kasar Philippines an ba da rahoton cewa fiye da mutane dari daya ne suka mutu a birnin Tacloban da ke gabar teku kadai, yayin da kasar ta fara tattara bayanan bannar da mahaukicyar guguwarnan da aka yi wa lakabi da Haiyan ta farma kasar.

Galibin gine gine hadi da filin jirgin saman birnin sun lalace, kodayake dai jiragen kai kayan agaji na sojoji suna isa birnin.

Harkokin sadarwa sun gamu da cikas abinda yasa aikin tattara bayanai yai matukar wahala.

Yanzu dai wannan mahaukaciyar guguwa da ke tafiya da ruwan sama ta durfafi Vietnam, amma masana sun ce karfinta zai ragu.

Karin bayani