An gaza daidaitawa game da nukiliyar Iran

Taron tattaunawa game da nukiliyar Iran
Image caption An gaza sasantawa a taron tattaunawa game da shirin nukiliya na Iran

An tashi tattaunawar da aka shafe kwanaki ukku ana yi a Geneva a game da shirin nan na nukiliya na Iran mai cike da rudami ba tare da cimma yarjejeniya ba - sai dai kuma an shirya za a koma zaman tattaunawar cikin kwanaki goma masu zuwa.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce an samu cigaba mai ma'ana ta fuskar tabbatar da cewa kasar ta Iran ba ta mallaki makaman nukiliya ba.

To amma ya kara da cewa an shafe tsawon lokaci ana takaddamar diplomasiyya.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya ce ran sa bai baci ba game da sakamakon tattaunawar, saboda akwai alamun za a cimma yarjejeniya a zaman da za a yi nan gaba,kodayake dai ya ce babu tabbacin hakan zuwa karshen tattaunawar.