Gwamnatin Nijar ta yi nasara a majalisa

Firayi-Ministan Nijar, Briji Rafini
Image caption Firayi-Ministan Nijar, Briji Rafini

A Nijar da alamun har yanzu gwamnatin Praminista Briji Rafini tana da farinjini - kamar dai yadda kuri'ar da 'yan majalisar dokoki suka kada a jiya ta nuna.

Gwamnatin ta samu kuri'u 70 daga cikin 113, dake nuna goyon bayan tsarin ayyukan da gwamnatin zata gudanar, daga yanzu zuwa 2015.

Arba'in da uku(43) daga cikin 'yan majalisar ne suka nuna adawa.

Gwamnatin ce da kanta ta nemi 'yan majalisar su bayyana ra'ayoyinsu game da ita, bayan ficewar jam'iyyar Moden-Lumana daga kawancen jam'iyyu masu mulki, da kuma cece-kucen da ya biyo baya.

Wasu daga cikin 'yan adawa majalisar sun zargi gwamnatin da yin magudi wajen zaben, ta hanyar saye wasu 'yan majalisar da kudi, zargin da magoya bayan gwamnatin suka musanta.