Kasashen duniya na agaza wa Philippines

Ta'adin mahaukaciyar guguwar Haiyan
Image caption Ta'adin mahaukaciyar guguwar Haiyan

Kasashen duniya sun kaddamar da wani gagarumin aikin kai dauki a Philippines domin agazawa mutane fiye da miliyan hudu, bayan bugawar mahaukaciyar guguwar Haiyan mai tafe da ruwa, wadda ta yi ta'adi a yankin tsakiyar kasar.

An yi amunnar dubban mutane sun hallaka.

Ana ta binne gawarwaki masu yawa a manyan ramuka.

Rundunar sojan Philippines din na ta jigilar ma'aikatan gaggawa da kayayakin da ake matukar bukata ta jiragen sama zuwa wuraren da lamarin ya fi shafa.

Jiragen saman Amirka na yaki su ma zasu bi sahu.

Tarayyar Turai ta bada agajin gaggawa na dala miliyan hudu.

Shugaban kasar, Benigno Aquino, ya ce da farko su na neman biyan bukatun wadanda suka tsira, musamman mutanen da suka jikkata.

Shugaban ya je birnin Tacloban da guguwar ta yi kaca-kaca da shi, inda ya ce za a bada fifiko wajen maido da wutar lantarki da kuma gyara hanyoyin sadarwa.