ASUU na ganawar janye yajin aiki

Zanga-zangar malaman jami'o'i a Nigeria
Image caption Zanga-zangar malaman jami'o'i a Nigeria

Kungiyar malaman jami'o'i ta Nijeria ASUU za ta yi wani taron 'ya'yanta don tattauna tayin da gwamnatin kasar ta yi musu a zaman da suka yi da shugaban kasa a makon jiya.

Kungiyar dai za ta yanke shawara a lokacin taron kan ko za ta janye yajin aikin da ta shiga sama da kwanaki dari da suka gabata.

Ko da yake kungiyar ta ASUU ba ta baiyana tayin da shugaban kasar ya yi mata ba, gwamnati na cewa ta na da kyakkyawan zaton za'a cimma matsaya tare da janye yajin aikin.

Ra'ayin 'yan Nigeria dai ya bambanta game da yajin aikin. Yayinda wasu ke kiran malaman da su daure su koma bakin aiki wasu kuwa cewa su ke kamata ya yi kungiyar ta dage kan bakanta har sai gwamnatin ta cika alkawurran da ta dauka na inganta ilimi a kasar.