An rage farashin lantarki a Ghana

Image caption Shugaba John Dramani Mahama

Hadaddiyar kungiyar kwadagon kasar Ghana, ta janye yajin aikin kasa baki daya da tayi niyar yi daga ranar 18 ga wannan watan bayan da gwamnati ta rage kudin wutar lantarki.

Gwamnatin kasar ta sanar da ragi daga kashi 78 cikin 100 na farashin wutar lantarki da ta yi zuwa kashi 58 cikin 100.

A cikin watan Satumbar da ya wuce ne, gwamnatin Ghana tayi karin farashin da kashi 78 cikin 100 kan wutan lantarki da kuma karinkashi 52 cikin 100 kan farashin ruwan fanfo.

Batun karin ya janyo kakkausar suka daga wajen al'ummar Ghana, wadanda suka ce zai kara musu wahalhalun rayuwar da suke fuskanta.

Karin bayani