Mutane miliyan daya na fama da yunwa a Nijar

Image caption Nijar dai kan fuskanci irin wannan matsalar kusan a kowace shekara.

Pirai Ministan Jamhuriyar Nijar ya ce mutane kimanin miliyan daya ne ke fuskantar barazanar yunwa sakamakon fari da ambaliyar ruwa a kasar.

A yayin wani zaman muhawara a majalisar dokokin kasar, Malam Brigi Rafini ya ce ba a samu amfani gona da yawa ba a daminar bana a kasar; wadda fiye da rabinta ke cikin hamadar Sahara.

Malam Brigi Rafini ya ce ana bukatar kashe Euro miliyan 84 daidai da dalar Amurka miliyan 112 domin magance matsalar.

Kasar ta Nijar dai ta fuskanci ambaliya ruwa a watannin baya ; wadda ta halaka mutane sama da 30, ta raba wasu dubu 200 da gidajensu ta kuma mamaye gonaki.

Karancin abincin da ake yawan samu a kasar dai na haddasawa kananan yara fiye da dubu 300 kamuwa da tamoua yayinda dubu shida daga cikinsu kan mutu a kowacce shekara.

Karin bayani