PDP ta dakatar da Oyinlola

Alamar jam'iyyar PDP
Image caption Alamar jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta dakatar da Mr Olagunsoye Oyinlola daga cikin Jam'iyyar.

Mr Oyinlola dai shi ne tsohon sakataren jam'iyyar, wanda ke cikin wadanda suka balle zuwa sabuwar PDP.

A makon jiya ne wata kotu ta tabbatar da zabensa a matsayin halattaccen sakataren jam'iyar.

Haka kuma Jam'iyar ta PDP ta dakatar da shugaban sabuwar PDPn Kawu Baraje, da mataimakinsa Sam Jaja da kuma Sanata Ibrahim Kazaure, mataimakin shugaban jam'iyar na kasa mai kula da shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Karin bayani