Ana zaman juyayi a Philippines

Image caption Mahaukaciyar guguwar ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane

Shugaban Philippines, Benigno Aquino, ya ayyana zaman juyayi a kasar sakamakon babban bala'in mahaukaciyar guguwa da aka yi wa lakabi, Haiyan, mai dauke da ruwa da ta yi kaca-kaca da kasar.

Ya ce manufar wannan ayyanawa ita ce a gaggauta bayar da agaji ga mutanen da suka tsira daga bala'in, sannan a samar musu da kayan amfanin yau-da-kullum cikin rahusa.

Mahaukaciyar guguwar dai -- daya daga cikin manya masifu da suka fadawa kasar --- ta kashe dubban mutane a tsibirin Leyte na birnin Tacloban kadai.

Har yanzu ba a kai ga zuwa wasu garuruwa da mahaukaciyar guguwar ta lalata ba don haka ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.

Karin bayani