An sako attajirin da aka sace a Sokoto

Image caption Alhaji Abu Dankure dai shi ne Sarkin Fadan Sarkin Musulmi

Majiyoyi daban-daban a birnin Sokoto na arewacin Najeriya sun ce an sako hamshakin attajirin nan da aka sace a garin ranar Laraba.

Kakakin 'yan sanda a jihar Sokoto DSP Almustafa Sani ya shaidawa BBC cewar an sako Alhaji Abu Dankure ne da yammacin ranar litinin bayan kwashe kwanaki biyar a hannun wadanda suka sace shi.

Sai dai ya ce 'yan sanda ba su da cikkakun bayanai kan yadda aka sako mutumin.

Wani mai magana da yawun iyalinsa ya ce an sako shi cikin koshin lafiya kuma ba wani kudin fansa da aka biya kafin sakin nasa.

Wasu 'yan bindiga ne suka sace Alhaji Abu Dankure a cikin motarsa lokacin da yake dawowa daga sallar Isha'i da daren ranar Laraba.

Karin bayani