'Tilastawa 'yan Nigeria karuwanci a Spain'

Image caption Wasu daga wadanda ke shiga karuwanci a Turai

'Yan sandan kasar Spain sun kama wasu mutane 25, wadanda suka ce suna fataucin mata daga Najeriyar, suna tilasta masu aikin karuwanci a kasar ta Spain ko a wasu kasashen Turai.

Ana kuma zargin gungun mutanen da aikata zamba da intanet, ta hanyar amfani da katunan bankin da suka sata.

'Yan sandan sun ce mutanen na zuwa ne su samu 'yan matan a Najeriya su yi masu dadin baki cewa zasu sa su a wata hanyar rayuwa da ta fi wadda suke ciki inganci, da samar masu aiki mai mutunci a Turai.

Ana zargin cewa su kan dauke su ne zuwa latin Amurka, daga can su shiga da su Faransa, inda daga canne kuma suke satar shigar da su kasar Spain.

'Batar da sawu'

A wani bangare na aikin samamen da suka kai, 'yan sandan sun kwace motoci 94 a Madrid.

Sun kwace wasu karin 26 tashar jiragen ruwa ta Valencia.

Bisa dukkan alamu gungun mutanen na shakare manyan motocin da giya da kuma akwatunan talabijin, amma sai su like motocin domin boye kayan dake ciki.

'Yan sanda sun gano kayayyakin da aka boye na kimanin euro miliyan 5 cikin motocin.

'Yan sandan sun hakikance cewa ta wannan hanyar shigar da kaya ta jiragen ruwa zuwa Lagos, ne suke satar shigar da kudaden da suka samu.

Wadanda aka kama za kuma a tuhume su da laifin aikata zamba ta intanet, ta hanyar satar katunan bankin jama'a suna juyar bayanan dake cikinsu.

A lokacin samamen, 'yan sandan Spain sun ce sun kubutar da wasu mata biyar daga hannun gungun mutanen.

'Yan sandan suka ce daya daga cikin matan tana ma da ciki, kuma lokacin da suka isa wurin, daya daga mutanen na kokarin zubar da cikin.

Karin bayani