Guguwar Haiyan ta afkawa Vietnam

Image caption Yanzu dai guguwar ta rikide zuwa wani hadari mai tsanani

Ruwa da iska masu karfin gasken da suka daidaita lardin Leyte na kasar Philippines tare da haddasa hasarar dubban rayuka sun afkawa lardin Quang Ninh na arewacin kasar Vietnam.

Kodayake mahaukaciyar guguwar mai hade da ruwa wadda aka yi wa lakabi da Haiyan ta rage karfi, tana tafe ne da iska mai gudun kilomita 150 a kowace sa'a lokacinda ta afkawa gabar ruwan lardin da safiyar ranar litinin.

Ana tsammanin samun ruwan saman mai karfi da ambaliya a babban birnin kasar Hanoi.

Rahotannin sun ce kawo yanzu mutane shida sun mutu.

Karin bayani