An soma taron hana daukar ciki a Afrika

Ana kokarin rage haihuwa a Afrika.
Image caption Ana kokarin rage haihuwa a Afrika.

Shugabannin gwamnatoci da kwararru kan lafiya na duniya na taro a Adis Ababa, babban birnin Ethiopia domin tattaunawa kan ba da cikakkiyar damar samun magungunan hana daukar ciki.

An shirya taron na kasa da kasa kan tsarin iyali ne tare da hadin gwiwar Gidauniyar Bill and Malinda Gates.

Gidauniyar ta ce mata fiye da miliyan dari biyu da ashirin da ba su son daukar cikin ne ba su da kafar samun magungunan na hana daukar ciki.

A cewar gidauniyar fiye da mata dubu 280 ne ke mutuwa sanadiyyar haihuwa a kowacce shekara a fadin duniya, kuma za'a iya ceton rubu'insu ta hanyar ba su magungunan hana daukar ciki.

Ministocin kasashe 20 ne ke halartar taron bisa kudirin habaka zuba jari kan samar da magungunan hana daukar ciki ga kasashen Afrika.