Mahaukaciyar guguwar Haiyan: Jiya da yau

Hotunan garuruwan Philippines da mahaukaciyar guguwar Haiyan ta yiwa barna.

Garin Anibong da ke kusa da birnin Tacloban
Bayanan hoto,

Hotunan Philippines da aka dauka ta sama na nuna irin barnar da mahaukaciyar guguwar ta yi a kwaruruwa irin su Tacloban da ke tsibirin Leyte da Guiuan, na lardin Gabashin Samar. Wannan garin Anibong ne da ke kusa da birnin Tacloban.

Bayanan hoto,

Jiragen ruwa a gabar Anibong kusa da birnin Tacloban, inda mahaukaciyar guguwar ta yi mummunar barna.

Bayanan hoto,

A garin Tacloban, birni mafi girma kan tsibirin Leyte, kimanin mutane 10,000 ne ake fargabar sun mutu.

Bayanan hoto,

Wadanda suka tsira sun fara laluba buraguzan gidajensu don ganin abubuwan da suka tsira.

Bayanan hoto,

Mahaukaciyar guguwar ta yi barna a filin saukar jiragen sama na Tacloban, inda ta rusa gine-gine, ta tumbuke bishiyu, tare da kifar da motoci.

Bayanan hoto,

Jiragen soji na iya sauka a yanzu dauke da kayan agajin da ake matukar bukata.

Bayanan hoto,

Guiuan na cikin garuruwan da mahaukaciyar guguwar ta fara sauka kuma tayi matukar barna.

Bayanan hoto,

An samu rahoton dibar ganima a wasu shagunan ajiya bayanda karancin abinci ya addabi mutane.