Masar tafi kowa danne hakkin mata

Matan Masar sun fi fuskantar danniya a kasashen larabawa
Image caption Matan Masar sun fi fuskantar danniya a kasashen larabawa

Wani bincike ya baiyana cewa Masar ce ta fi kowacce kasar larabawa danne hakkin mata, sanadiyyar tashin hankalin da ya biyo bayan hambarar da gwamnatin Husni Mubarak.

Binciken da gidauniyar Thomson Reuters ta gudanar ya gano cewa wariyar jinsi, yawaitar kaciyar mata da kuma karuwar tasirin masu kishin Islama sun jefa Masar matsayi na karshe cikin kasashe 22 na larabawa da aka bincika.

Tsibirin Comoros - inda mata ke rike da kaso 20 na mukamin minista a gwamnati - ita ce kan gaba wurin kare hakkin mata.

Binciken dai ya bibiyi ra'ayin kwararru kan hakkin jinsi 330 ne da ke cikin kasashe 22 na kungiyar kasashen larabawa da kuma Syria, wacce ta na cikin wadanda suka kafa kungiyar amma aka dakatar da ita shekaru biyu da suka wuce.