'Yan sandan Nigeria zasu samu horo

'Yan sandan Nigeria sun yi kaurin suna wurin keta hakkin bil'adama
Image caption 'Yan sandan Nigeria sun yi kaurin suna wurin keta hakkin bil'adama

Gwamnatin Nigeria ta kaddamar da wani sabon shirin horar da 'yan sandan kasar kan kare hakkin bil'adama.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Nigeria ce za ta bayar da horon na gwaji a jihohi biyar na kasar da kuma birnin tarayya, Abuja.

Za'a horar da 'yan sandan nan game da kare hakkin bil'adama wurin kama wanda ake zargi da laifi, tsare shi da kuma yi masa tambayoyi.

'Yan sandan Nigeria dai sun yi kaurin suna wurin keta hakkin bil'adama.