Rikicin PDP na kara ruruwa

Image caption Shalkwatar PDP a Abuja

A Najeriya, bangaren sabuwar PDP da ya bijire wa shugabancin Bamanga Tukur ya bayyana dakatarwar aka yi wa wasu shugabanninsa su hudu da cewa mataki ne na kama-karya, kuma alama ce da ke nuna cewa lokaci ya yi da kowa zai kama gabansa.

A ranar Litinin ne dai bangaren PDP karkashin Bamanga Tukur ya sanar da wannan dakatarwa bisa zargin mutane hudun bisa da yi wa jam'iyyar zagon kasa, bayan wata kotu ta tabbatar da halalcin daya daga cikinsu, wato Mr Olagunsoye Oyinlola a matsayin halaltaccen sakataren jam'iyyar na kasa.

A martaninsa, Mr. Olagunsoye Oyinlola ya ce dakatarwar ta sabawa doka tunda babu wanda ya tuntube shi don ya kare kansa daga zargin da ake masa kafin ace an dakatar da shi.

Ya kuma ce idan da gaske ne don me mahukuntan PDP suka kasa dakatar da gwamnoni da 'yan majalisu na jam'iyyar da suka balle suka kafa sabuwar PDP.

Shi kuwa, Ambasada Ibrahim Kazaure, ya ce babu mamaki don shugabannin PDP sun karya doka don kuwa halinsu ne.

A cewarsa,PDP ba so take a sasanta rikicin da ke cikinta kuma su sun daura aniyar rigima da PDP.

Karin bayani