'Mutane 2500 ne suka mutu a Philippines'

Jama'a a Philippines
Image caption Jama'a a Philippines

Shugaban kasar Philippines Benigno Aquino ya ce gwamnatinsa na cigaba da kokarin gano adadin mutanen da suka rasu a mahaukaciyar guguwar Haiyan wadda ta yi kaca-kaca da wasu sassan kasar kwanaki biyar da suka wuce.

Ya ce alkaluman farko da jami'ai a yankin suka fitar wadanda suka nuna cewa mutane dubu goma ne suka rasu ya yi yawa matuka.

Alkaluman baya bayan nan sun yi kiyasin mutane dubu biyu da dari biyar ne suka rasu.

Rahotanni daga Philippines din na cewa yanayin tsabta ya tabarbare a wuraren da guguwar ta yiwa mummunan ta'adi.

An ruwaito cewa ruwan da jama'a ke amfani da shi ya gurbace da najasa, lamarin da ke sanya karuwar hadarin yaduwar cututtuka.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar talafin kudi sama da dala miliyan 300 domin taimakawa mutanen da guguwar Haiyan ta shafa.

Da ta ke kaddamar da gidauniyar jami'ar hukumar ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta ce aikin bada agajin yana tafiyar hawainiya saboda katsewar hanyoyi da kuma wasu matsaloli da suka shafi sufuri.

Wani mai magana da yawun kungiyar abinci ta duniya Greg Barrow, ya shaidawa BBC cewa kayan agaji na tafe.

Ya ce kungiyoyin agaji sun koyi darasi daga abinda ya faru a Japan na ambaliyar tsunami shekaru biyu da suka wuce

Jiragen dakon kaya na sojin Philippines dana Amurka suna ta jigilar sauka filin jiragen sama.

Sai dai wakilin BBC yace har yanzu babu alamar taimako da ya isa ga mutane dubu dari biyu dake zaune a birnin wadanda ke tsananin bukatar abinci da ruwan sha da kuma matsuguni.

Karin bayani