'Yan tawayen Syria sun kafa "gwamnati"

'Yan tawayen Syria na neman kwace mulki daga Bashar Assad
Image caption 'Yan tawayen Syria na neman kwace mulki daga Bashar Assad.

Gamaiyar kungiyoyin 'yan adawar Syria ta kafa majalisar zartarwa mai wakilai tara domin kasancewa abin da ta kira gwamnatin wucin gadi wadda aka dorawa alhakin gudanar da yankunan da yan tawayen suka kame.

Wani mai magana da yawun kungiyar yace abin da za'a fara baiwa fifiko shine kafa jagorancin kananan hukumomi da kuma samar da muhimman bukatu da suka hada da Ilmi, lafiya, ruwan sha da kuma wutar lantarki.

Da yake magana jim kadan bayan baiyana sunayen 'yan majalisar zartarwar Pirai ministan rikon kwarya na hadakar majalisar 'yan adawar Ahmad Toumeh yace wannan wani muhimmin lokaci ne ga Syria.

Ya ce: "Wannan rana ce mai matukar tarihi ga Syria wanda muka dade tsawon shekaru hamsin muna jira. Rana ce mai tarihi ga jama'ar Syria."