Amurka ta ce Boko Haram 'yan ta'adda ne

Image caption 'Yan Kungiyar Boko Haram

Amurka ta saka kungiyar Boko Haram da ta Ansaru a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, wannan matakin nada mahimmanci kuma shine kadai hanyar da gwamnatin Nigeria za ta bi wajen murkushe ayyukan 'yan kungiyar.

Wannan matakin zai kasance umarni ga duk wasu cibiyoyi da hukumomi na Amurkar su toshe duk wata kafar huldar kasuwanci da mu'amala ta kudi da ta shafi kungiyar ta Boko Haram da kuma Ansaru.

Ya zama babban laifi a karkashin dokar Amurka a bayar da duk wani taimako ga kungiyar bisa wannan sabon matakin.

Kungiyar dai na kai hare-hare ne arewacin Najeriya inda ta ce tana son kafa tsarin Shari'ar Musulunci; an kuma dora mata alhakin mutuwar dubban mutane.

Dama kungiyar kiristoci ta Nigeria ta matsawa Amurka ta sa Boko Haram cikin jerin kungiyoyi 'yan ta'adda. Kodayake a wasu lokutan kungiyar ta kaiwa kiristocin hari, mafi yawan wadanda 'yan kungiyar suka kashe musulmi ne.

Kawo yanzu ba wata alama da ke nuna dakarun sojin Nigeria na samun nasara kan 'yan Boko Haram. Kowanne mako mayakan kungiyar na kashe farar hula a a arewa maso gabashin kasar sannan kuma ana yawan zargin sojin da keta hakkin bil'adama a yankin.

Karin bayani