Hawaii ta amince da auren jinsi daya

'Yan Madigo
Image caption 'Yan Madigo a Amurka

Majalisar dattawa a jihar Hawaii ta Amurka ta zartar da dokar da ta halatta aure tsakanin masu jinsi iri daya.

Ana sa ran Gwamna Neil Abercrombie daya daga cikin masu babatun nuna goyon baya ga aure tsakanin masu jinsin iri daya zai rattaba hannu kan dokar ranar Laraba, abinda zai sanya Hawaii din zama jiha ta 15 a Amurka da ta halatta aure tsakanin masu jinsin guda.

Masu sharhi a Jami'ar Hawaii sun ce wannan yunkurin zai sa tsibirran na yankin Pacific su zamo wurin ziyara da shirya bukukuwan aure tsakanin masu jinsin iri daya - abinda zai kawo wa jihar miliyoyin daloli na kudin shiga a 'yan shekaru kadan masu zuwa.

Shugaba Obama wanda aka haifa a Hawaii ya jinjinawa majalisar dokokin bisa amincewa da dokar.

Karin bayani