Za a kara yawan agaji a kasar Philippines

Kasar Philippines
Image caption Kasar Philippines

Gwamnatin Philippines ta ce za ta kai ga duk wadanda mahaukaciyar guguwar nan da aka yiwa lakabi da Haiyan ta shafa don agaza musu.

A wani martani da ya mayar game da shan suka, sakataren majalisar ministocin kasar Rene Almendras ya ce, illar da mahaukaciyar guguwar nan ta ranar Juma'a wadda ta shafi mutane miliyan 11 ta yi a ta tayarwa da mahukuntan hankali matuka.

Mr Rene Almendras yace kasar na fuskantar kalubale mafi girma yayin da ta ke kokarin samar da ruwa da abinci da kuma magunguna domin taimakawa wadanda suka tsira daga bala'in.

Wani babban kwamandan sojin Amurka a kasar ta Philippines Brigadier Janar Paul Kennedy, ya shaidawa BBC cewa wani jirgin daukar kaya na Amurkar ya isa tsibirin Leyte don raba kayan agajin.