Amurka za ta sa Boko Haram cikin 'yan ta'adda

Image caption A baya dai Amurka ta ki amincewa da yin hakan duk kiran aka yi mata na tayi hakan.

Jami'ai a kasar Amurka sun ce ma'aikatar harkokin wajen kasar na shirin sa kungiyar nan mai fafutuka da makamai ta Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad ko Boko Haram da ke Najeriya a sahun kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen ketare.

Wannan yunkuri, zai kasance wani umarni ga duk wasu cibiyoyi da hukumomi na Amurkar su toshe duk wata kafar huldar kasuwanci da mu'amala ta kudi da ta shafi kungiyar ta Boko Haram.

Idan an yi haka zai zamo babban laifi a karkashin dokar Amurka a bayar da duk wani taimako ga kungiyar.

Kungiyar dai na kai hare-hare ne arewacin Najeriya inda ta ce tana son kafa tsarin Shari'ar Musulunci; an kuma dora mata alhakin mutuwar dubban mutane.

Karin bayani