An takaita zirga zirga a jihar Anambra

Zabe a Najeriya
Image caption Za a gudanar da zaben Gwamna a Anambra karkashin tsauraran matakan tsaro

A Najeriya, ranar Asabar ne za 'a gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra dake kudancin kasar.

A sakamakon haka, jami'an tsaro da hukumar zabe ta kasa, wato INEC, sun bayar da sanarwar hana zirga-zirga a duk fadin jihar, daga karfe shida na yammacin ranar Juma'a zuwa karfe shida na safiyar ranar Lahadi.

Hukumomin biyu dai sun ce sun dauki wannan mataki ne domin tabbatar da doka da kuma oda a lokacin zaben Gwamnan da kuma ganin cewa an yi zabe mai inganci.

Sai dai jam'iyyar adawa ta APC ta tsargu da sahihancin matakin takaita zira zirga a lokacin zaben.