Mutane 40,000 sun gudu Nijar daga Najeriya

Image caption Yawan masu ficewa daga Nigeria ya karu bayan sanya dokar ta-baci

Rikicin kungiyar Boko Haram a Nigeria ya tilastawa mutane kusan dubu 40 tsallakawa kan iyaka zuwa jamhuriyar Niger.

A watan Yuni, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa 'yan gudun hijirar Nigeria 6,000 sun tsallaka zuwa Niger, amma yawan jama'ar ya karu tun bayan da gwamnatin Shugaba Jonathan ta kara zafafa yunkurinta na murkushe 'yan Boko Haram.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a alkalumansa da ya fitar ya ce akwai 'yan gudun hijira 37,332 yanzu haka a Niger, kuma daga cikinsu 29,000 'yan Jamhuriyar Niger ne sai sauran kuma 'yan Nigeria ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen ya nunka sau uku na irin abinda aka shiryawa don bada taimako ga 'yan gudun hijira.

A ranar Laraba ne Amurka ta saka kungiyar Boko Haram da ta Ansaru a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewar 'yan gudun hijirar sun watsu a sansanoni 20 a Niger musamman a yankin Diffa.

Karin bayani