An daure magoya bayan Mursi shekaru 17

'Yan sanda sun kama dubunnan magoya bayan Mursi a Masar.
Image caption 'Yan sanda sun kama dubunnan magoya bayan Mursi a Masar.

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru 17 a kurkuku ga magoya bayan hambararren shugaba Muhammad Mursi 12, bisa laifin ta da tarzoma a watan Oktoba.

Kotun ta samu mutanen ne da laifukan da suka hada da barnar kayan hukuma tare da zagon kasa a lokacin zanga-zangar da dalibai suka jagoranta a jami'ar al-Azhar.

Kotun da ke birnin Cairo ta yanke wa masu laifin belin dala dubu tara-tara zuwa lokacin da za su kammala daukaka kara.

Gwamnatin Masar da sojoji ke marawa baya ta kame dubunnan magoya bayan kungiyar Muslim Brotherhood ta shugaba Mursi tun bayan hambarar da mulkinsa a watan Yuli.