'Yan sanda sun kashe mayaka 6 a Pakistan

'Yan bindiga na tada kayar baya a Pakistan
Image caption 'Yan bindiga na tada kayar baya a Pakistan.

'Yan sanda a Pakistan sun ce sun kashe akalla mutane shida da su ke zargin 'yan bindiga ne a wani hari da suka kai daren jiya a garin Karachi da ke kudancin kasar.

Sun ce sun kwato wasu rigunan kai harin bakin wake da kuma mota shake da bama-bamai daga wurin mutanen.

Harin dai na zuwa ne daidai lokacin ibadar Ashura da 'yan Shia kan yi kowacce shekara a yankin.

A baya dai an sha kai wa 'yan Shi'ar hare-hare.

Mahukunta sun rarraba dubunnan 'yan sanda a fadin Pakistan tare da toshe layukan wayar salula a wasu muhimman birane domin dakile shirin mahara.