Agaji ya fara isa Philippines

Birnin Tacloban ne mahaukaciyar guguwar tafi barnatawa.
Image caption Birnin Tacloban ne mahaukaciyar guguwar tafi barnatawa.

Babban kwamandan sojin Amurka a Philippines ya ce gudunmawar da Amurka ke baiwa wadanda mahaukaciyar guguwar Haiyan ta yiwa barna ta dara duk wata gudunmawar bala'i da ta taba yi a baya.

Birgediya Janar Paul Kennedy ya shaidawa BBC cewa jirgin ruwan Amurka mai daukar jiragen sama George Washington zai isa tsibirin Leyte, abinda zai bada damar kara jigilar kayan agaji da jiragen helikopta ninki uku.

Haka kuma an bude hanyar mota mai shiga birnin Tacloban inda mahaukaciyar guguwar tafi barna.

Image caption Mutanen Tacloban sun fara fid da rai da samun agaji.

Gwamnatin Philippines dai na cigaba da shan suka game da matakan da take dauka bayan afkuwar mahaukaciyar guguwar ta Haiyan.

Babbar jaridar kasar, Manila Bulletin ta ce mutanen Tacloban sun fara fid da rai da samun dauki, yayin da wata jaridar ke tambayar anya shugaba Benigno Aquino zai iya aikin kuwa?

Gwamnatin Philippine ta amsa cewa barnar da guguwar ta yi ta zarta duk wani tanadinta sai dai ta ce duk masu bukatar tallafi zasu samu.

Shugabar bada agaji ga wadanda annoba da bala'i suka afka musu ta majalisar dinkin duniya Valerie Amos ta ce ita ma dai ta raina yunkurin majalisar na tallafawa mutanen da mahaukaciyar guguwar ta afkawa.