Majalisar Nigeria ta dage ganawa da hafsoshi

Ihejirika
Image caption Janar Ihejirika shugaban rundunar sojin Nigeria

Majalisar wakilan Nigeria ta dage ganawar da ta shirya yi da manyan hafsoshin tsaro daga Alhamis zuwa Larabar makon gobe.

Majalisar ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron domin jin bayani game da jihohin Borno, Yobe da Adamawa masu fama da tarzoma gabannin amincewa da kara wa'adin dokar-ta-baci a yankin.

Sai dai kuma majalisar ta dage zaman bayan da wasu daga cikin manyan hafsoshin tsaron suka sanar da ita cewa tafiyar aiki ta fitar da su daga Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria.

Tuni dai majalisar dattawan Nigeria ta amince da karin wa'adin watanni shida ga dokar-ta-bacin yayinda majalisar wakilan ke dakon sauraron bayani daga jami'an tsaron kafin daukar mataki kan kudirin.