'Yan Ethiopia 23,000 sun mika wuya a Saudiyya

Bakin haure na barin Saudiyya bayan cikar wa'adi
Image caption Bakin haure na barin Saudiyya bayan cikar wa'adi

Kimanin 'yan Ethiopia 23,000 ne suka mika kansu ga hukumomin Saudiyya tun bayan cikar wa'adin da aka debawa bakin haure na barin kasar a makon jiya.

Korar bakin hauren dai ta haifar da tarzoma a Riyadh, babban birnin kasar inda mutane biyar suka mutu.

Mahukuntan Saudiyya sun ce su na kokarin rage rashin aikin yi ne da kaso 12 cikin 100 na al'ummar kasaqr ke fama da shi.

Kimanin 'yan ci rani daga Afrika miliyan tara ne ke aiki a Saudi Arabia.

Jami'ai sun ce kusan rabin masu aikin karfi da sauran kananan ayyuka a Saudiyya 'yan Afrika ne.