Masu cutar suga na kukan tsadar magani

Allurar Insulin
Image caption Cutar sukari bata -da maganin da ake amfani da shi a warke baki daya

Yau ce ranar yaki da ciwon sukari ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a duk shekara domin kara fadakar da jama'a game da ciwon na sukari, da kuma halin da wadanda ke fama da cutar ke ciki.

Wasu alkaluma na Hukumar lafiya ta Duniya na cewa mutane kimanin miliyan 350 ne ke fama da cutar ta Suga a fadin duniya

Da dama daga cikin irin wadannan mutane dai sun fito ne daga kasashen Afirka.

Cutar bata da maganin da ake amfani da shi a warke baki daya, sai dai mutum ya rika shan magani na tsawon rayuwarsa.

Yayin da ake bikin wannan rana wasu masu fama da cutar a Najeriya sun koka da tsadar maganin cutar inda suka ce kamata ya yi gwamnati a dukkanin matakai ta rika samar da wannan magani kyauta domin saukakawa talakawa.