'Yan Philippines na neman tudun mun tsira

mazaunan Tacloban na kokarin ficewa
Image caption mazaunan Tacloban na kokarin ficewa

Dubunnan mutane na kokarin ficewa daga birnin Tacloban, inda mahaukaciyar guguwar Haiyan ta yi barna.

Mutane sun jeru a bakin titin zuwa filin saukar jiragen sama, inda suke fatan za su samu jirgin da zai fitar da su.

A tashar jiragen ruwan birnin ma wasu dubunnan sun cika suna neman mafita.

Kungiyar tallafi ta Save the Children ta ce ba zata iya kai tallafi wasu yankunan ba sai ranar Asabar, fiye da mako guda bayan saukar mahaukaciyar guguwar.

Wakilin BBC da ke Tacloban ya ce ana fargabar tabarbarewar tsaro a birnin yayinda mutanen da suka shiga matsi ke neman abinci.