An kai hari a garin Dansadau a Zamfara

Abdulaziz Yari, Gwamnan Zamfara
Image caption Abdulaziz Yari, Gwamnan Zamfara

A Najeriya wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari a garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce, sun kai harin ne da zummar kwato wasu tarin shanu da aka kwace a wurinsu, shanun da aka ce sato su suka yi.

An ce maharan sun rinka yin harbe harbe a iska, kuma sun kona ofishin 'yan sandan garin na Dansadau.

Sai dai kuma rahotannin na cewa tuni aka tura karin jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro.

Al'ummar garin na cikin zaman dar dar bayan aukuwar lamarin.