EFCC ta kama 'ya'yan Sule Lamido

Image caption Gwamna Sule Lamido

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta damke 'ya'yan gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido su biyu maza bisa zargin hannu a zambar naira biliyan 10.

Hukumar EFCC ta tabbatarwa da BBC kama 'ya'yan gwamnan, inda tace ta kama su ne a ci gaba da binciken da take yi, bayan kama Aminu Sule Lamido a shekara ta 2012 dauke da dala dubu 50 a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira.

A wancan lokacin, Aminu Sule Lamdo ya bayyana a gaban wata babbar kotu a Kano inda aka yanke masa hukunci.

Matakin na EFCC na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin gwamnan jihar Jigawan da kuma uwar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Kawo yanzu dai, babu martanin da Alhaji Sule Lamido ya mayar a kan kama 'ya'yansa biyu maza.

Karin bayani