An fara taron Commonwealth a Sri Lanka

Taron Commonwealth a Sri Lanka
Image caption Shugaban Sri Lanka Mahinda Rajapaksa da matarsa Shiranthi na maraba da Yarima Charles na Ingila.

An bude taron shugabannin kungiyar Commonwealth a Sri Lanka, yayinda ake cigaba da cece-kuce game da dacewar a kasar a matsayin masaukin taron.

Kasashen Canda, India da Mauritius sun kauracewa taron saboda fushin rashin amincewar Sri Lanka da kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa game laifuffukan yakin da ake zargin gwamnatin da aikatawa lokacin da ta samu nasarar murkushe 'yan tawayen Tamil Tigers a 2009.

Pirai ministan Birtaniya David Cameron na halartar taron amma ya na ziyarar jagororin 'yan Tamil da ke arewacin kasar a yini na farko na taron.

Ya ce hakan zai yayata irin abubuwan da suka faru a Sri Lanka kuma zai ba shi damar sukan keta hakkin bil'adama.