'Dole Kenyatta ya gurfana gaban ICC'

Image caption Kenyatta da Ruto

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yaki amince da yinkurin dakatar da shari'ar Shugaban Kenya da mataimakinsa a kotun hukunta laifuka ta duniya wato ICC.

Matakin ya biyo bayan bukatar shugabannin kasashen Afrika wadanda suka bukaci a dakatar da shari'ar Shugaba Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto.

Kasashen takwas cikin 15 na kwamitin tsaro sun kauracewa kada kuri'a, abinda yasa bukatar ba ta samu nasara ba.

Ana zarginsu da hannu wajen tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar a 2007, inda mutane 1,200 suka mutu.

Karin bayani