Sojojin Nijeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Rundunar sojojin Najeriya ta bakwai da ke fafatawa da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal Jihad, da aka fi sani da Boko Haram, a Maiduguri ta jihar Bornon Najeriya ta ce ta kashe wasu 'yan kungiyar.

Rundunar sojan ta ce ta hallaka 'yan kungiyar ta Boko Haram ne su ashirin tare da fatattakar su daga wani sansaninsu a jihar ta Borno a wani farmaki da sojan suka kaddamar da hadin gwiwar sojin sama na kasar.

A sanarwar da rundunar sjojin ta bakwai ta fitar ta ce ita ma ta rasa sojanta daya wasu kuma sun sami raunuka a artabun.

Karin bayani