Taron gwamnoni a Sokoto

Gwamnonin jihohin Najeriya
Image caption Taron bitar shi ne na biyu na kungiyar gwamnonin

Wasu gwamnonin jihohin Najeriya na taron bita a Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar.

Suna taron ne karkashi tutar Kungiyar Gwamnonin Najeriya Wadda Rotimi Ameachi na jihar Rivers ke shugabanta.

Masana daga ciki da wajen kasar na halartar daron inda suke gabatar da kasidu kan matsalolin kasar da yadda yakama a magance su.

Sai dai Gwamnoni goma sha biyu kawai ke halartar taron daga cikin tala tin da shida da aka gayyata.

Hakan na kara tabbatar barakar da ke kuniyar gwamnonin tun bayan da aka zabi shugabanni biyu kowanne na ikrarin shi ne halattacen Shugaban.

Bangaren Rotimi Amechin da kuma na gwamnan jihar Plateau Jonah Jang.