Mutane 100 sun mutu a rikicin Sudan

Sudan
Image caption Har yanzu kabilu na gwabzawa da juna

Rahotanni daga Sudan sun ce kazamin fadan da aka tafka tsakanin kabilun dake kan iyaka na yammacin yankin Darfur yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 100 a 'yan kwanakin nan.

Gidan rediyon gwamnati ya ruwaito cewa rikicin tsakanin kabilun Misseriya da na Salamat a wuraren garin Umm- Kukhun ya cigaba a ranar Asabar.

Wasu rahotannin na cewa rikicin ya shafi sojojin kasar Chadi wadanda suke sintiri tare da sojojin Sudan akan iyakar.

Majalisar dinkin duniya tayi gargadin cewa fada tsakanin kungiyoyin biyu ya sa dubun dubatar mutane sun rasa matsugunnasu a daukacin yankin.