An sako Bafaranshen da aka sace a Katsina

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya sanar da cewa an sako wani Injiniya Bafaranshe da aka yi garkuwa da shi a arewacin Najeriya.

Injiniyan mai suna Francis Collomp mai shekaru sittin da uku yana gudanar da aikin samar da wutar lantarki ne ta hikimar amfani da iska a jihar katsina dake arewacin Najeriyar lokacin da 'yan kungiyar Ansaru suka sace shi a watan Disambar bara.

Kungiyar Ansarun ta ce ta yi garkuwa da shi ne a matsayin ramuwar gayya kan yunkurin da Faransa ta yi a wancan lokaci na fatattakar mayakan kungiyar Islama a Mali.