Za a kammala taron kungiyar Commonwealth

Pira Ministan Birtaniya David Cameron a Sri Lanka
Image caption Pira Ministan Birtaniya David Cameron a Sri Lanka

Yau za a kammala taron kungiyar Commonwealth, kuma kasar Sri Lanka mai karbar bakunci na fatan maida hankali kan batun sauyin yanayi da basussuka.

An dai yi ta zazzafar takaddama da kasar Birtaniya kan batun kare hakkin bil adama.

A jiya ne dai shugaba Mahinda Rajapakse ya yi watsi da kiran da Pirayim Minista David Cameron yayi na gudanar da wani bincike na kasashen duniya game da zargin aikata miyagun laifukan yaki a zagayen karshe na yakin basasar kasar.

Ba dai a sa ran bayanan bayan taron daga shugabannin kungiyar Commonwealth za su kunshi batun wannan takaddama kai tsaye.

Mr Rajapakse ya ce, za su yi nazari tare da gudanar da bincike kan yakin da aka shafe shekaru 30 ana yi.