An nemi Hodgson ya zama Kociyan Jamus

Image caption An nemi Roy Hodgson ya zama Kociyan Jamus

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya ce tsohon kociyan Jamus Franz Beckenbauer shine ya hanashi zama kociyan Jamus, a lokacin da aka nemeshi.

Hukumar kwallon kafa ta Jamus ta tunkari Roy Hodgson da mukamin a shekarar 1998.

Amma Roy Hodgson ya ce tsohon kociyan Jamus din Beckenbauer na ganin dan Ingila zai iya toshe damar 'yan Jamus na hawa mikamin.

Hodgson mai shekaru 66, ya taba jagorantar Switzerland zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya a 1994 da kuma gasar cin kofin Nahiyar Turai a 1996.

Karin bayani