Gwamnonin sabuwar PDP sun gana a Sokoto

Taron gwamnonin jam'iyar PDP 7 a Najeriya
Image caption Taron gwamnonin jam'iyar PDP 7 a Najeriya

Gwamnonin nan bakwai na sabuwar PDP sun yi wata ganawa ta sa'oi hudu da tsakar daren jiya a fadar gwamnatin jahar Sakkwato.

Ganawar wadda aka ce ita ce ta yanke shawarar karshe kan ko su ci gaba da kasancewa a PDP ko kuma a'a , an yi ta ne tare da Kakakin Majalisar Dokokin kasar Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Shugaban Sabuwar PDPn Abubakar Kawu Baraje, da wasu 'yan majalisar dattawa uku.

Sai dai bayan fitowar su , gwamnonin ba su yi bayani kan sakamakon zaman ba, amma daya daga cikin su ya shaidawa BBC cewar za su bayyana sakamakon ganawar wani lokaci a ranar Lahadi.

Jam'iyyar adawa a APC dai tana zawarcin gwamnonin bakwai.