Za a sake wasan cin kofin Ingila da aka dakatar

Image caption Ranar Alhamis za a buga wasan da aka dakatar na kofin Ingila

Hukumar Kwallon kafa ta Ingila ta tabbatar da cewa wasan da aka dakatar na ranar Asabar na cin kofin Ingila tsakanin Colwyn Bay da kuma Altrincham za a sake yinsa ranar Talata.

An dai dakatar da wasan a mintuna 83 inda a lokacin Altrincham na da ci biyu 2-0 yayin da Alkalin wasa Mark Ackerman ya ji rauni.

Colwyn Bay dai sun ki amincewa da Jami'ai biyu da aka ce su ci gaba da busa wasan.

A dokar Hukumar idan wasan farko aka daga shi ko aka bar shi kafin cikar mintina 90 kuma babu kulob din da yake da laifi to sai an sake shi kafin ko kuma ranar Alhamis.

Karin bayani