Dalibai sun yi zanga zanga a Yamai

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaban NIjar Mahamadou Issoufou

A Nijar dubban daliban makarantun sakandare a birnin Yamai sun yi zanga zanga a yau inda suka yi ta kone-konen tayoyi.

Daliban sun ce za su cigaba da kaurace wa azuzuwansu har nan da ranar Laraba, domin kokawa da yadda suka ce hukumomin ilimi na jahar na yiwa bangaren ilimin rikon sakainar kashi.

Daliban sun koka da rashin isassun dakunan karatu da malamai, da kuma kayayakin aiki.

Jami'an tsaro sun kama wasu daliban kamin daga baya su sako su.

Hukumomin ilimi na birnin Yaman dai sun ce suna kokarin shawo kan matsalolin daliban.