Ana gware tsakanin FIFA da SAFA kan wasa

Image caption Zargin sayar da wasa ya sa takunsaka tsakanin FIFA da SAFA

Hukumar Kwallofa ta duniya da kuma Huumar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu SAFA na gware kan zargin binciken ma'aikatan Hukumar SAFA da ake zargi da sayar da wasa.

FIFA dai ta ce za ta dauki ragamar binciken daga wajan Hukumar SAFA din.

Gwamnatin Afrika ta kudu ta kaddamar da bincike kan zargin da ake yi cewa Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudun ta bada hadin kai ga Kungiyar Footbal 4U wadanda Hukumomi a Singapore suka yankewa hukuci kan sayar da wasa a 1995 da kuma a Finland a 2011.

Da farko dai Jami'an Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudun su biyar; har da shugaba na wancan lokacin Kirsten Nematandani, an dakatar da su watan Disambar bara.

Dakatar war ta biyo bayan rahoton FIFA wanda ya ce ma'aikatan sun hada kai da wasu wajan nada Alkalin wasan da ya busa wasannin sada zumunta na Bafana-Bafana guda biyar a 2010.

Karin bayani