An kashe mutane 22 a ofishin jakadancin Iran

Image caption Da alamu za a samu karin wadanda suka mutu

An samu fashewar abubuwa biyu masu karfi a ofishin jakadancin Iran dake Lebanon, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane fiye da 22, wasu kuma da dama suka samun raunuka.

Wani babban jami'in Iran, Sheikh Ibrahim Ansari na daga cikin wadanda suka mutu.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda motoci suka yi kaca-kaca ga kuma gawarwaki a warwatse a yayinda hayaki ya turnuke yankin da Shi'a keda rinjaye a birnin Beirut.

Wakilin BBC ya ce harin nada nufin aika sako ga gwamnatin Iran da kuma kungiyar Hezbollah masu goyon bayan gwamnatin Syria.

Jakadan Iran a Lebanon ya zargin Isra'ila da kaddamar da wannan harin, zargin da Isra'ilar ta musanta.

Karin bayani